Uncategorized

Asalin abin da yasa kotu ta haramta wa ado Gwanja yin waka….

Babbar kotun jihar Kano Mai Lamba biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a A’isha Mahmud ta bada umarnin a kamo mata mawaƙi Ado Isa Gwanja.

Kadaura24 ta rawaito Kotun ta kuma haramta masa waƙa har sai ‘yan sanda sun kammala bincike a kansa.

Idan za’a iya tunawa a bara lokacin da mawaƙin yayi wata waƙa mai suna “WAR” zauran malaman Kano sun shigar da shi ƙara a kotun Shari’ar Musulunci dake Bichi ta hannun lauya Barr. Sulaiman Gandu, saboda a cewar su waƙar akwai kalaman batsa a cikinta kuma zata iya ɓata tarbiyyar yara a Kano.

A

wancan lokacin kotun ta bada izini a kamo mawaƙi ado Gwanja, amma sai ya garzaya babbar Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba biyar ya kuma karɓo takardar da ta hana kotun ta kama shi a wancan lokacin.

A zaman ta na wannan rana kotun ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a A’isha Mahmoud ta bada umarnin a kama Ado Gwanja, sannan ta ce ta haramta masa yin kowacce irin waƙa har sai ‘yan sanda sun kammala bincike kan zargin da malaman Kano suka yi masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button