Uncategorized

Ki fa’dawa Mijinki Al’ummar na fama da Yunwa, Sarkin kano Aminu ado ya Fa’dawa matar Shugaba Tinubu a lokacin da ta Kai Masa ziyara.

Maimartaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero ya tura Sako ga Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ta hannun Uwargidan sa Sen Oluremi Tinubu a ziyara da kaiwa Maimartaba Sarkin. Fadar sa.

Maimartaba sarki yace muna da hanyoyin tura sako ga Shugaban kasa da yawa Amma kasancewar ki Uwargidan sa kinfi kowa kasanci dashi.

Al’umma suna kawo mana kukan su na tsananin rayuwa da ake ciki a Wannan lokaci, ya kamata Gwamnati ta duba hanyoyin saukakawa Al’umma.

Mun samu kiraye kiraye daga al’umma Akan dauke wasu manyan ma’aikatu daga Birnin Abuja zuwa Lagos kamar wani bangare na CBN da FAAN , al’umma basu gamsu da Wannan yunkurin ba, ya kamata Gwamnati ta duba sosai don tabbatar da masalahar al’umma, Idan muka Gwamnati tana da hujja mai Karfi sai tayi bayani yadda al’umma zasu gamsu.

Muna fata Wannan sako zai isa ga Maigirma Shugaban kasa.

Daga Isma’il Lamido..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button